Gwamnati jihar ta rufe kasuwar ne bayan wata tirela mai dauke da kaya ta fada cikin mahautar garin, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum shida.
Alhaji Ibrahim Jiddah wanda shi ne chairman na babbar kasuwar shanun garin Aba ya ce an kai masa labarin fadawar tirelan a cikin kasuwar, da yadda aka samu asarar rayuka da dukiya.
An kuma shaida masa cewa za a mayar da su wani wuri amma har yanzu hakan ba ta samu ba.
Amma wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun ce wajen da aka mayar da su cikin daji ne kuma basu saba da wurin ko kuma gane yanayin wurin ba, musamman yadda sha’anin rashin tsaro yake a kasar. Sun nuna damuwar su cewa a halin yanzu mutane basu tsira a cikin gari ba ballantana a jeji.
‘Yan kasuwar sun kara da cewa a halin da suke ciki har yanzu gwamnati bata turo masu sojojin da za su kare su ba. Suna jiran gwamnati to je tayi masu abinda ya kamata saboda matsalar rashin tsaro da kuma babbobinsu dake daji.
Saurari rahoto cikin sauti daga Alphonsus Akoroigwe: