Seif al-Islam Gadhafi Da Yayansa Mohammed Basa Hanu

'Yan tawayen Libya suke dannawa ta inda sojoji masu biyayya ga Gadhafi suke a Tripoli.

'Yan tawayen Libya suke dannawa ta inda sojoji masu biyayya ga Gadhafi suke a Tripoli.

Sojoji masu biyayya ga shugaba Moammar Gadhafi sun fafata da ‘yan tawaye a wasu wurare nan da can, cikin birnin Tripoli a daren jiya litinin.

Sojoji masu biyayya ga shugaba Moammar Gadhafi sun fafata da ‘yan tawaye a wasu wurare nan da can, cikin birnin Tripoli a daren jiya litinin, yayinda ake samun rahotanni anga dan shugaban Gadhafin, kuma mutuminda ake ganin shine zai gaji ubansa, Seif al-Islam, yana yawonsa babu tsangwama a birnin na Tripoli, ba kamar yadda ‘yan tawaye suka bada labarin sun tsare shi ba.

‘Yan jarida da dama ciki har da wakilan tashar talabijin ta CNN d a na kamfanin dillancin labaran faransa sun ce sunga Sei-al-Islam a safiyar yau Talata a wurare daban daban a cikin babban birnin. Wan nan sabanin rahotanni da shugabannin ‘yan tawaye har da kotun sauraron kararrakin manyan laifuffukan yaki dake Hague, duk sunce Seif-al-Islam, wadda ake caji da laifukan yaki yana hanun ‘yan tawaye.

Haka kuma wasu majiyoyi daga kusoshin ‘yan tawaye suna cewa babban dan shugaba Gadhafi Mohammed shima ya tsere daga daurin talala da suka yi masa. Amma dansa na uku yana hanu.

Ahalin yanzu kuma shugaban majalisar gudanawa ta ‘yan tawaye, Mustafa Abdel jalil, yace ‘yan tawayen basu san ko shugaban Libyan yana cikin kasar ba. Yace za’a yi wa shugaba Gadhafi adalci idan suka kama shi, ya kara da cewa “nasara ta hakika zata tabbata ne” idan suka kam aGadhafi.

Jalil ta gaskanta cewa har yanzu basu kama birnin Tripoli baki daya ba.Yace sojoji masu biyayya ga shugaba Gadhafi suna da iko na kashi 10-15 na babban birnin ciki har da fadar shugaban kasa da ake kira Bab-al-Aziziya.