Ganin an fara samun sauki daga rikicin Boko Haram, ‘yan Janhuriyar Nijar da su ka tsere zuwa gida lokacin da tashin hankalin na Boko Haram ke tsanani, sun fara dawowa Najeriya ganin an fara samun kwanciyar hankali a kalla a wasu sassan Najeriya.
Wakilinmu a Janhuriyar Nijar Haruna Mamman Bako ya ruwaito wani daga cikin masu niyyar sake komawa Najeriya mai suna Malam Sani sun a shirin komawa Najeriya ne saboda an samu kwanciyar hankali a wuraren da su ke neman abin zaman gari a kasar. Ya ce dawowa gida Nijar tamkar dora ma ‘yan’uwa lalura ne ga ‘yan uwa. Gashi kuma ba su saba da zama gidan ba kamar yadda su ka saba da zama Najeriya.
Malam Sani ya ce wasu da su ka koma Najeriya sun yi ta buga masu waya su na gaya masu cewa al’amura sun kyautatu kuma har ma wasunsu ma sun sami wasu wuraren sana’ar da su ka fi na da samu. Don haka, a cewar Sani, ba makawa za su koma Najeriya.
Shi kuma Malam Abubakar ya alakanta kyautatuwar al’amuran ne da irin matakan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke daukawa, ya na mai nuna gamsuwa da yadda manyan sojojin Najeriya na yanzu keg aba-gaba wajen yaki da Boko Haram.
Your browser doesn’t support HTML5