Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Na Ziyarar Kwanaki Uku a Faransa


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Lokacin Da Ya Kama Hanyar Tafiya Afrika ta Kudu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Lokacin Da Ya Kama Hanyar Tafiya Afrika ta Kudu

A yau Litinin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fara wata ziyarar kwanaki uku a kasar Faransa bayan da takwaran aikinsa Francois Hollande ya mika mai goron gayyata.

Wata sanarwa da mai baiwa shugaba Buhari shawara kan hulda da jama’a da ‘yan jarida, Femi Adesina, ya ce mai baiwa Buhari shawara kan harkar tsaro, Major-General Babagana Monguno mai ritaya, da manyan jami’ai a ma’aikatun tsaro da kudade da noma da harkokin wajen Najeriya, na daga cikin wadanda suka rufawa shugaba Buhari baya a wannan ziyara.

A cewar sanarwar ta Adesina, irin tawagar da Buhari ya tafi da ita, alama ce da ke nuna cewa tattaunawa shugabanin biyu za ta ta’allaka ne kan yadda za a karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu a fannonin da suka hada da tsaro da huldar kasuwanci da kuma saka hannayen jari.

Ana sa ran da yammacin yau ne Hollande zai gana da Buhari a fadarsa ta Alysee da ke Paris inda har ila yau ake kuma tunanin shugaban na Najeriya zai gana da ministan tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian da ministan kudi Michel Sapin da sauran manyan jami’an gwamnatin Faransa.

A ranar Laraba mai zuwa ake sa ran Buhari zai dawo Najeriya bayan kammala wannan ziyara.

Ibrahim Ka'almasi Garba ya tambayi Malam Aminu Sule mai fashin baki a harkar diplomasiya kan tasirin wannan ziyara ga kuma yadda hirarsu ta kaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG