Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Najeriya da ‘Yan Jarida Na Zargin Juna


Wasu sojojin Najeriya masu shigara da kara
Wasu sojojin Najeriya masu shigara da kara

Dakarun Najeriya da ‘yan jaridun kasar sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda kowane bangare ke gudanar da aikinsa.

Yayin da sojojin kasar ke zargin ‘yan jaridu da rubuta labaran da ka iya bata sunan Najeriya a idon duniya, ana su bangaren ‘yan jaridun sun zargi sojojin da ba da hadin kai yayin da suke neman labaran da za su rubuta rahotanninsu.

Wannan takaddama ta kaure ne yayin da sashen dakarun sojin na runduna ta 23 da ke Yola ke jagorantar wani taro na masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro.

“Muna so mu kawar da yadda kuke ba da labaran da za su iya bata sunan kasarmu, akwai yadda ya kamata ku manema labarai ku rubuta rahotannin ku, dole ne mu hada hanu wajen kare mutuncinmu Najeriya.” In Ji Brigadier- General Rogers Ibe Nicholas, shugaban sashen kula da kyautata dangantaka tsakanin fararen hula da sojoji na runduna ta 23.

Sai dai ana su bangaren, ‘yan jaridar sun zargi sojojin ne da rashin samar musu da bayanai domin su hada rahotonsu.

“A matsayi na dan jarida, ana bukatar na samar da sahihan bayanai, matsalar ba a wurinmu ta ke ba, mukan fuskanci matsaloli kamar barazana daga jami’an tsaro, har da ku sojoji, kuma dole ne mu fadi abinda ya faru, tun da mu jama’a ke saurare su ji daga garemu.” In ji wani dan jarida da ya halarci taron.

Ga karin bayania wannan rahoton da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz ya aiko mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG