Saudiyya Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2034 - FIFA

FIFA confirm Saudi Arabia as 2034 World Cup hosts

FIFA ta kuma amince da gasar cin kofin duniya na shekarar 2030, wanda za a gudanar a kasashe shida kuma a nahiyoyi uku, inda za a gudanar da wasanni uku na farko a Argentina, Paraguay da Uruguay.

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta tabbatar da kasar Saudiyya a hukumance a matsayin wacce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2034 a gasar kwallon kafa ta maza.

Saudiyya ce ‘yar takara daya tilo da ta nemi daukar nauyin gasar, kuma ta samu yabo daga mambobin FIFA sama da kasashe 200.

Sun halarci wani taro ta yanar gizo da shugaban hukumar Gianni Infantino ya shirya a birnin Zurich a ranar Laraba.

Matakin ya zo a hade da amincewa da dan takar daya tilo da zai karbi bakunci gasar cin kofin duniya ta 2030.

FIFA ta kuma amince da gasar cin kofin duniya na shekarar 2030, wanda za a gudanar a kasashe shida kuma a nahiyoyi uku, inda za a gudanar da wasanni uku na farko a Argentina, Paraguay da Uruguay.

Kasar Uruguay da ke kudancin Amurka za ta cika shekaru 100 da karbar bakuncin wasan cin kofin duniya na farko da aka buga a 1930.