Wannan jerin jadawalin yana zuwa ne bayan shafe wata guda ana buga wasanni, inda Argentina ta lashe kofin Copa America bayan da ta doke Colombia, yayin da Sifaniya ta lashe European Championship bayan ta doke Ingila.
Ingila ta koma ta hudu, bayan da tawagar Brazil da ta kasa tabuka abun kirki a gasar cin kofin Copa America da aka yi a Amurka, ta koma ta biyar.
Venezuela, wacce ta kai wasan kwata-fainal a gasar Copa America ta zama kasar da ta fi samun ci gaba a jadawalin, bayan da ta tsallake matsayi 17 ta zama 37, yayin da Turkiyya da ta kai wasan kwata-fainal a gasar Euro ta tsallake matsayi 16 ta zama ta 26 a duniya.
Maroko tana matsayi na 14, yayin da ta samu koma baya da matsayi biyu bayan da ta kai wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta 2022, wacce ita ce ta daya a jadawalin tawagar kwallon kafar maza ta Afirka.
Amurka ta samu koma baya da matsayi 5 zuwa ta 16, inda ta ke kan gaba da matsayi daya kan abokiyar hammayarta Mexico.
Japan tana matsayi na 18 a duniya, inda tafi kowace a tawagar kwallon kafa ta Asiya.
Ga jerin kasashe 10 da ke kan gaba a sabon Jadawalin da aka fitar:
1 - Argentina
2 – France
3 – Spain
4 – England
5 – Brazil
6 – Belgium
7 – Netherlands
8 – Portugal
9 – Colombia
10 - Italy
Dandalin Mu Tattauna