A wani yunkuri na magance matsalolin da ke addabar jama’a a Najeriya, Nijar, Chadi, Kamaru, Burkina Faso da Mali, Saudiyya ta sanar da shirinta na karbar bakuncin wani “babban” taro wanda zai mayar da hankali kan yadda za a tallafa wa kasashen yankin.
Taron a cewar wata sanarwa da hukumomin Saudiyya suka fitar a ranar Juma’a, za a yi shi ne tare da hadin gwiwar Kungiyar Hadin kan kasashen Musulmi ta OIC a ranar 26 ga watan Oktoban 2024.
“Kasashen yankunan Sahel da na Tafkin Chad sun jima suna fuskantar matsaloli cikin sama da shekaru goma.
“Suna fuskantar kalubale da dama, wadanda sukan shafi fannonin rayuwar al’umar yankin ciki har da na tattalin arziki.” Sanarwar wacce Muryar Amurka ta samu kwafi ta ce.
“Bugu da kari, janyewar ruwan Tafkin Chadi, wanda ke samar wa da miliyoyin mutane hanyoyin dogaro, ta kara dagula al’amura, lamarin da ke bukatar tallafin gaggawa.” Sanarwar ta kara da cewa.
A wani kiyasi da ta yi, Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum miliyan 33 ne suke bukatar taimako da kariya a yankin ciki har da mutum miliyan 11 da aka raba da muhallansu da kuma masu gudun hijira a yankunan na Sahel da Tafkin Chadi.
Wannan taro wanda zai wakana karkashin hadin gwiwar jagorancin Cibiyar Tallafa wa ta Sarki Salman (KSrelief) da Kungiyar OIC da ofishin tallafa wa al’uma na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) da kuma ofishin kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) “ya kuduri aniyyar hada tallafi a kuma shata hanyoyin da za a kare rayukan al’uma, fararen da dabbaka hanyoyin da za a taimakawa mutane don su fita daga kangin wahalhalun da suke ciki.”
“Ina kira ga daukacin mambobin OIC, kungiyoyi masu ba da tallafi, da kawaye na ketare, da su yi amfani da wannan dama su taimaka da kudade da sauran hanyoyi don taimakawa wajen kyautata rayuwar al’umomin da ke wadannan yankuna.” In ji Dr. Abdullah Al Rabeeah, Shugaban kungiyar KSrelief.