Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Ta'addanci Da Ke Da Alaka Da Al-Qaeda Sun Tsallaka Zuwa Arewacin Najeriya


Yan bindiga
Yan bindiga

A cewar rahoton masana a cibiyar Clingendael, kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin da aka yi ittifakin suna da alaka da al-qaeda suka rika tsallakowa daga yankin arewacin jamhuriyar Benin sun samu mafaka a gandun dajin gwamnati dake Kainji, daya daga cikin mafiya girma a Najeriya.

Wani rahoto da aka fitar a ranar Laraba yace, mayakan masu ikrarin jihadi da suka jima suna addabar kasashen yankin sahel mai fama da tashe-tashen hankula sun kafa sansani a shiyar arewa maso yammacin Najeriya bayan da suka ketaro daga jamhuriyar Benin, wani sabon salo da kungiyoyin ke dauka a kasashe masu arziki dake gabar tekun yammacin Afirka.

A cewar rahoton masana a cibiyar Clingendael, wacce ta gudanar da bincike mai zurfi akan yankin sahel, a shekarar data gabata, kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin da aka yi ittifakin suna da alaka da al-qaeda suka rika tsallakowa daga yankin arewacin jamhuriyar Benin dake fama da rikici tare da samun mafaka a gandun dajin gwamnati dake Kainji, daya daga cikin mafiya girma a Najeriya, inda sauran kungiyoyi ‘yan bindiga suka samun mafaka.

Mazauna yankin dake kusa da gandun dajin sun shaidawa kamfanin dillacin labarai na AP cewar an rufe dajin, wanda ke zama gadun da adadin zakuna ke raguwa cikin sauri a yammacin Afirka tsawon fiye da shekara guda, saboda barazanar tsaro daga kungiyoyin ‘yan bindigar dake addabar makwabtan kauyuka da hanyoyi.

A cewar John Yarima, wanda ke zaune kusa da gandun dajin a garin New Bussa: “a da, wurin tamkar cibiya ce ta baki ‘yan yawon bude ido, amma yanzu, da wuya mutane ke wucewa ta wurin. ba zaka iya bin ta hanyar data nufin gandun ba. abune mai matukar hatsarin, gaske.”

Kars de Brujine, daya daga cikin mawallafa rahoton kuma babban mai bincike yace, dadewar kungiyoyin ‘yan bindiga a cikin gandun dajin ita ce alamar farko ta alaka tsakanin masu tsattsarar akida na gida Najeriya dake tada kayar baya tsawon shekaru a shiyar arewacin kasar da ‘yan bindiga masu alaka da al-Qaeda a yankin sahel, dake kudancin sahara.

Ya kara da cewar, kasancewar a wurin ya bada dama ga tsageru suyi ikrarin samun nasara a dukkanin kasashen 2, dake fama da miyagun hare-hare a ‘yan shekarun baya-bayan nan.

-Reuters

A saurari karin bayani daga Hassan Maina Kaina:

Kungiyoyin Ta'addanci Da Ke Da Alaka Da Al-Qaeda Sun Tsallaka Zuwa Arewacin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG