Saudi Arabia Ta Tabbatar Da Mutuwar Kashoogi

Yarima Mohammed bin Salman na Saudi Arabia

Saudi Arabia tace sakamakon binciken farko da ta gudanar a kan bacewar dan jaridar Saudiyar nan Kamal Kashoogi, ya nuna ya mutu a ofishin jakadancinta a Istanbul bayan fada da ya yi da mutane da ya same su a wurin, a cewar ma’aikatar labaran kasar.

Wata sanarwa da ofishin babban lauyan gwamnatin Saudi Arabia ya fitar, da telbijin kasar ta sanar da safiyar yau Asabar, sanarwar na cewa tuni an kama ‘yan kasar Saudi Arabia 18 nasaba da mutuwar Kashoogi kana an kori mai baiwa kotun masarautar Sauiya shawara, Saud al-Qahtani da kuma mataimakin shugaban hukumar tattara bayanan sirrin kasar Ahmed Assiri.

Babban lauyan gwamnatin yace ana nan ana ci gaba da bincike a kan mutuwar Kashoogi

Kamfanin dillancin labaran kasar ya kuma ce Sarki Salman ya bada umarnin kafa kwamitin ministoci karkashin jagorancin yarima Mohammed domin sake kafa hukumar tattara bayanan sirrin kasar.

Kalaman na yau Asabar sune na karon farko da gwamnatin Saudiya ta tabbatar da mutuwar Kashoogi.

A baya Turkiya ta fada cewa an kashe Kashoogi a ofishin jakadancin Saudiya a Istanbul a ranar biyu ga watan Oktoba, amma Saudia Arabia tayi ta musantawa wannan zargi..