Duk da cewa tarihi ya nuna akwai abokantaka da hulda mai kyau a tsakanin kabilun Tiv da Fulani, an samu barkewar tashin hankali a tsakanin wadannan al'ummomi biyu har sau 14 a shekarar 2015 a yankunan kananan hukumomin dake kudanciun Jihar Taraba.
Tara daga cikin wadannan tashe-tashen hankulan sun yi munin da ya kai ga zub da jini.
Kwararru a fannin shiga tsakani da sasanta al'ummopmin dake rikici da juna, sun alakanta rikicin kabilanci na jihar Taraba da bambancin siyasa, wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dama da hasarar dukiya maras iyaka.
Haka kuma, wadannan rikice-rikicen sun tilasta ma jama'a daga kowane bangare neman mafaka a wasu kananan hukumomi ha rda jihohi makwabta.
Shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya mai zaman kanta ta jami’ar Amurka a Najeriya Dr, Abubakar Abba Tahir, ya yi Allah wadai da tashe-tashen hankula tsakanin al’ummomin biyu wadanda yace tun fil’azal abokai ne kuma 'yan'uwan juna.
Wakilin sashin Hausa Sanusi Adamu wanda ya yi nazarin rikicin Tivi da Fulani a jihar Taraba a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.
Your browser doesn’t support HTML5