Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Jihar Taraba Ta Amince Da zaben Sabon (Sarki) Kpanti Zing


Nadin sarauta a arewacin Najeriya
Nadin sarauta a arewacin Najeriya

Alhaji Suleiman Ibrahim Sambo ya sami amincewar gwamnatin jahar Taraba a matsayin Saki (Kpanti) Zing.

Gwamnatin Jihar Taraba ta amince da zaben sabon Kpanti Zing, Alh. Suleiman Ibrahim Sambo bayan tuntubar juna da Majalisar Masarautar Gargajiyar ta.

Alh. Suleiman Ibrahim Sambo zai maye gurbin marigayi Kpanti Zing Alh. Abbas Ibrahim Sambo wanda ya rasu ranar ashirin da hudu ga watan nan a turmitsitsin da ya auku lokacin aikin hajjin bana.

A hukumance, amincewa da zaban Alh. Suleiman Ibrahim Sambo ya kawo adadin sarakunan da suka taba rike mukamin zuwa bakwai, tun daga zamanin mulkin mallaka.

Wakilinmu Sanusi Adamu ya rubuto cewa bayaga taya sabon sarkin murna, gwamnan jihar Taraba Arch. Darius Dickson Ishaku ya kalubalance shi da ya tabbatar da dorewar zaman lafiya a masarautar, wadda ita kadai ce a jihar da ba ta fuskantar rikicin kabilanci, siyasa ko na addini ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG