Kwamitin sauraren korafe-korafen cin zarafi da ake zargin rusasshiyar rundunar ‘yan sanda ta musamman da ke yaki da miyagun laifuka wato SARS, da ke zama a jahar Filato na ci gaba da sauraren shaidu kan korafe-korafen da ke gabanshi.
Wasu da suka gabatar da korafin cin zarafi a gaban kwamitin sun bayyana irin ukubar da suka ce sun sha a hannun ‘yan sandan na SARS. Kama daga mai zargin ‘yan SARS sun nakasa shi da harbi da kuma bugu bisa zargi mara tushe zuwa mai cewa kaninsa ya mutu sanadiyyar harbin da ‘yan sandan SARS su ka yi masa a kai – da dai sauran zarge zarge masu karkada hanji.
Shugabar kwamitin, Mai Shari’a Philomena Lot, ta ce sun karbi takardun korafe korafe fiye da sittin daga jama’a, wadanda ke zargin cewa ‘yan sanda, musamman ma na rundunar SARS, da aka rusa daga baya, sun gallaza masu tare da tauye masu hakki babu gaira babu dalili.
Barista Yirvams Chamsan Jips, wanda ke halartar zaman kwamitin, ya ce yana da yakinin cewa wadanda suka gabatar da koke koken za su sami adalci.
Ga Zainab Babaji da cikakken rahoton ta sauti: