NIGER, NIGERIA - Sultan Sa’ad Abubakar wanda yake jawabi wajen bikin nadin sarauta tare da mika sanda ga sabon Sarkin Sudan na Kontagora a Jihar Neja, Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu na biyu a karshen wannan mako, ya ce suna gudanar da addu’o’i na musamman domin ganin an gudanar da wannan zabe cikin kwanciyar hankali.
Sabon Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu na biyu wanda shi ne na bakwai a jerin sarakunan masarautar ta Kontagora da ta samu asali daga Shehu Usman Danfodio ya ce za su yi kokarin kamanta adalci a wannan mulki, sannan ya bukaci hakimansa da daggatai dama masu unguwanni da su tabbatar sun sanya idanu kan jama’a musamman a wannan lokaci da ake fama da miyagun mutane.
Gwamnan Jihar Nejan Alhaji Abubakar Sani Bello wanda ya mika sandar mulkin ga sabon sarkin ya bukaci sarakunan Najeriya da su ba da gudummuwar da za ta taimaka wajen ganin an yi babban zaben kasar cikin nasara.
Sauari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5