Shugaba Brack Obama na Amirka da matarsa Michele sun ziyarci sarauniyar Ingila Elizabeth talatan nan. Bayan da aka sarauniyar tayi maraba dasu aka karama su da arba'in bindiga arba'in da daya a yayinda suke tsaye a matakalal fadar, da shi shugaba Obama da matarsa Michele da sarauniya Elizabeth da miniyan Yarima Phillip, da Yarima Charles da matarsa gimbiya Camilla. Obama da Michele da sarauniyar da mijinta da yarima Charles da matarsa duk sun tsaya akan matakalar fadar a lokacinda wata rundunar soja ta Scots ta rera taken Amirka. Tunda farko shugaba Obama da matarsa sun gana da ango da amarya Yarima William da gimbya Kate a asirce
Bayan da suka ci abincin rana shugaba Obama ya halarci bikin ajiye furanin kalo a Westminster Abbey sa'anan ya gana da Prime Ministan Ingila David Cameron da matarsa Samantha. Laraba nan idan Allah ya yarda shugaba Obama zai gana da Prime Ministan Ingila a hukunce. Ana sa ran shugabanin biyu zasu tattauna yadda al'amurra suke a Afghanistan da Libya da kuma batutuwan tattalin arziki. Ana kuma sa ran shugaba Obama zai gana da shugaban masu hamaiya ed Millband..
Sarauniya Elizabeth ta gaiyaci Obama da matarsa liyafar cin abincin dare. Ziyarar kwanaki biyu da shugaba Obama ke yi a London wani bangare ne na ziyarar kasashen turai guda hudu da yake yi.
A wata sanarwar hadin gwiwa da jarida Times of London ta buga talata nan, shugaba Obama da Prime Minista Cameron sunce baya ga cewa dangantaka tsakanin Amirka da Ingila ta musamma ma ce, tana kuma da muhimmanci sosai.