Mahaukaciyar guguwar teku data ratsa birnin Joplon a jihar Missouri nan Amirka a ranar lahadi ta kashe fiye da mutane dari. Jami'an dake nazarin yanayi sunce wannan guguwa, kila ta zama mafi muni da Amirka ta gani tun cikin kusan shekaru sittin da suka shige. A ranar lahadi da maraice guguwar ta apkawa birni Joplin, ta rushe gidaje da gine gine, tayi awon gaba da motoci da tuge itatuwa. Hukumomi sun baiwa mutane kashedin mintoci ashirn da hudu kafin guguwar ta apkawa birnin. Haka kuma mahaukaciyar guguwar ta lalata wata asibiti, data sa ala tilas aka kwashe majinyata daga cikinta. Ta kuma yi kaca kaca da wani jirgin sama mai saukar angulu dake ajiye a kusa da asibitin. Litinin masu aikin ceto suka ta neman wadanda kila sun makale a karkashin rusasun gine gine, to amma kuma sai wannan yunkuri nasu yayi kicibis da ruwan sama kamar da bakin kwarya. Jami'ai sun kiyasta cewa guguwar ta yiwa akalla kashi ashirin da biyar daga cikin dari na birnin Joplin wanda ke da kimamin mutane dubu hamsin barna. An bada rahoton cewa guguwar tayi juyawar kilomita maitan da sittin da biyar cikin sa'a guda.
A watan jiya mahaukaciyar guguwar teku hade da ruwan sama kamar ta bakin kwarya suka kashe fiye da mutane dari uku a jihohin kudancin Amirka. Jihar Alabama, ita tafi dandanawa inda aka bada rahoton cewa fiye da mutane maitan guguwar ta kashe.
Shugaba Barack Obama, wanda a halin yanzu yake ziyarar wasu kasashen turai, yace a ranar lahadi idan Allah ya kaimu, zai kai ziyara jihar Missouri. A yayinda yake magana a birnin London, yayi alkawarin cewa gwamnatin taraiyar zata taimakawa mutane yankin farfadowa da kuma taimaka musu sake gina birnin Joplin.