Shugaban Amurka Barack Obama ya kai gajeriyar ziyara a wani karamanin kauyen Ireland inda aka haifi kakanninsa, ya gaida daruruwan mazauna kauyen da suka nuna kaulin ziyarar da ya kai asalinsa. Mr. Obama da mai dakinsa Michelle sun tashi zuwa kauyen ne ta jirgin Helicopter daga Dublin babban birnin kasar, zuwa Moneygall a kauyen heartland yau Litinin. Jami’an kauyen ne suka tarbi shugaba Obama da kuma wani danginsa na nesa dan kasar Ireland, Henry Healy dan shekaru ashirin da shida da haihuwa. An haifi kakan kakan kakansa, Falmouth Hearney a Moneygall daga baya ya kaura zuwa Amurka a shekara ta dubu da dari takwas da hamsin lokacin ana tsananin yunwa a Ireland. Dan shekaru sha tara ya isa birnin New York daga nan ya zauna a Ohio domin neman ingancin rayuwa. Mr. Obama ya gano asalinsa na kasar Ireland ne lokacin da yake kamfen neman zabe a shekara ta dubu biyu da takwas. Mr Obama ya yi ta murmushi yayinda shi da mai dakinsa suke shan hannun mutanen kauyen da suka rika kada tuta a bayan wani shinge da aka kafa inda suka tsaya na tsawon sa’oi domin ganin shugaba Obama da mai dakinsa. Mr. Obama ya kuma shiga wata ‘yar bukka domin dandana wata irin barasa. Daga nan ya koma birnin Dublin domin ci gaba da ziyarar da ya fara tun farko inda ya gana da shugaba da kuma firaministan kasar.
Shugaban Amurka Barack Obama ya kai gajeriyar ziyara a wani karamanin kauyen Ireland inda aka haifi kakanninsa