Sanata Ahmad Lawal ya ce matakin sojan da aka dauka a game da al'amarin Boko Haram ba ya magani.
WASHINGTON, DC —
Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin cewa akwai bukatar dawo da sadarwar wayar salula a jahar Borno don hakan zai taimaka wajen bayar da labarai cikin gaggawa da samun dauki, hakan nan kuma za a samu raguwar mutanen da ke zuwa wasu garuruwa domin yin waya wadanda a wasu lokuta kan shiga haduran da ke rutsawa da rayukan su. Shi ma dan majalisar dattaban Najeriya mai wakiltar jahar Yobe Ahmad Lawal ya tada wannan magana a gaban majalisar domin ya ja hankalin gwamnati tarayya kan bukatar yin garambawul game da yadda take tinkarar dawo da zaman lafiya a arewa maso gabas. A tattaunawar su da wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu el-Hikaya, Sanata Ahmad Lawal ya bayyana hujjojin shi kamar haka:
Your browser doesn’t support HTML5