Mai fashin baki, Ishaya Buba Bajama, yace wannan shirin zai iya samar da dubban ayyukan yi, da samar da wadatar kayan abinci da bunkasa tattalin arzikin yankin arewacin Najeriya, inda aka fi dogara a kan noma.
A cikin wannan makon ne Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa zai zuba karin jari na sama da dala miliyan dubu 34 a tattalin arzikin Najeriya nan da shekarar 2017. Cikin fannonin har da na aikin gona, wanda Alhaji Aliko Dangote ya bayyana a zaman "kashin bayan tattalin arziki."
Alhaji Aliko Dangote ya kuma ce jarin da zasu zuba a fannin aikin gona, burinsa shi ne na samar da ayyukan yi ga dubban 'yan Najeriya, a bayan ciyar da jama'a, domin kuwa za a iya kara yawan masu aiki a fannin na noma daga dubu 26 da ake da su yanzu zuwa dubu 750.
Ga cikakken bayanin da malam Ishaya Buba Bajama yayi game da wannan shiri na Dangote.