Samun Daidaita Alamuran Siysa a Syria ne Zai Kawo Karshen ISIS - Obama

Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama yace za'a sami galaba kan kungiyar da larabawa suke kirantaDaesh, ita kuma ta kiran kanta ISIS idan aka sami daidatuwar harkokin siyasa a Syria.

Shugaban yace lamarin zai dauki shekaru, kuma yace ba za'a sami cikakkiyar nasara ta kawarda maboyarsu ba, har sai an sami wani daidaito ta fuskar siyasa a Syria.". shugaban ya furta haka ne a taron kolin kasashe da suke yankin Asiya da Pacific da ake yi a kasar Phillipines.

Haka nan shugaban ya tabo batun taron koli da zummar wanzar da zaman lafiya a Syrian da za'a nan gaba. Yace shawarwarin zasu gano kungiyoyin 'yan hamayya wadanda zasu kasance a bangaren gwamnatin wucin gadi, kamin a yi zabe, ko kafa sabuwar gwamnati.

Shugaban na Amurka yace akwai wani abu daya tabbas gameda makomar Syria anan gaba. Shugabanta na yanzu bashi da wani gurbi a sabon shirin ci gaba da tafiyar da harkokin kasar.

Shugaba Obama yace tilas Rasha da Iran su dauki wani muhimmin matsaya akan yadda suke cigaba da tallafawa Assad domin babu yadda zai ya ci gaba da mulkin kasar. Su yi tunane ko zasu yi aiki tareda hukumomin kasa da kasa wajen ceto kasar Syria amma ba da Al-Assad ba.