Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ba Zata Tura Sojojin Kasa Su Yaki ISIS Ba - Obama


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaba Barack Obama na Amurka yace zai zama kuskure Amurka ta tura sojojinta na kasa domin murkushe mayakan sakai na ISIS.Yaki karbar kiraye kirayen da ake yi masa cikin gida da kuma ketare, na daukan sabbin matakai masu karfi bayan harin ta'addancin da aka kai a birnin Paris.

A wani taro da manema labarai da yayi a dai dai lokacinda suke kammala taron koli na kwana biyu da aka yi a birnin Antalya dake kan gabar Bahar Rum, Mr. Obama ya kira kungiyar ISIS a zaman "Iblis," ya kara da cewa Amurka zata zafafa matakai da take dauka, amma ba zata canza dabaru ko manufofin kasar kan wannan yakin ba.

Mr. Obama ya ce harin da 'yan ta'adda suka kai a birnin Paris "mummunar al'amari ne da ya maida hanun agogo baya" a fafatawa da kungiyar ta ISIS, duk da haka yace Amurka ba zata tura sojojin kasa masu yawa zuwa yankin ba.

Yace "wannan ba ra'ayinsa ne shi kadai ba,harma da masu bashi shawara na kud da kud sojoji da fararen hula. Yace ba wai don sojojin Amurka ba zasu iya gamawa da su ba ne, amma don Amurka tana gudun sake gani ko nanata abunda ya faru lokacin da ta mamaye Iraqi.

Amma Sanata Dianne Feinstein, 'yar jam'iyyar shugaba Obama, jiya Litinin, ta bayyana matukar damuwa kan matakan da Amurka take dauka ahalin yanzu wajen tunkarar ISIS.

XS
SM
MD
LG