Jiragen yakin sama na kasar Faransa sun farma sansanin kungiyar ISIS dake Raqqa lugudan wuta har ma suka lalata wani wurin horaswa.
Wata sanarwa daga dakarun sojojin Faransa tace kimanin jirage goma ne suka kai hare-hare tare da jefa bamabamai ashirin akan wuraren dake da mahimmanci ga kungiyar,
Hare-haren su ne mafi yawa da Faransa zata kai kan kungiyar ISIS cikin Syria kuma sun biyo bayan harin ta'adanci ne da ya faru ranar Jummai da ta gabata wanda ita kungiyar ISIS ta dauki alhakn kaiwa. Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 130 kana wasu kusan dari hudu suka jikata.
Jiragen sun tashi ne daga kasar Jordan da hadadiyar daular Larabawa ranar Lahadi da yamma kuma sun kai hare-haren ne kafada da kafada da dakarun Amurka.
Tun farko shugaban Faransa Francois Hollande ranar Jummai ya alakanta hare-haren da aka kai kasarsa da yaki