Samarwa Da Dalibai Wadatattun Muhalli

Cincirindon Dalibai a wajen zanga zanga 12, ga Oktoba 2015

Ko me ke kawo matsalar muhalli a wasu jami’o’I a Najeriya, kan wannan batun ne muka tambayi, Mallam Kabir Sufi Sa’id na Kwalejin share fagen shiga jami’ar dake Kano.

Inda muka tambayeshi shin wannan matsala ce ta Arewacin Najeriya kawai ko kuwa ta duka Najeriya ce? Me ya kamata a yi ne a magance wannan matsala?

Mallam Kabir yayi bayanin cewa samun matsalar muhalli ba ya rasa nasaba da yadda wasu halayya da ‘dalibai keyi lokacin da suka kama gida dake ba a cikin makaranta ba, hakan yasa mutane ke kaucewa samarwa da dalibai muhalli a wajen makaranta.

A bangaren gwamnati kuma har yanzu ana amfani da tsari irin na da, inda yanzu yawan dalibai ya karu sosai kuma gwamnati bata fadada makarantun ba hakan kuwa shi ke kawo cunkozo da rashin jin dadi ga duk masu karatu.

Wanann matsala ce da ta shafi kasa baki ‘daya ba Arewacin Najeriya kadai ba, duk wanda ya gama makarantar jami’a shekaru 20 da suka gabata, to tabbas ya san da wannan matsalar ta karancin dakunan kwana domin da daddiyace.

Saurari cikakkiyar hirar da Mallam Kabir Sufi.