Wani kamfani mai suna “Glassdoor” yakan zakulo ayyuka da su kafi kasuwa a kasashen duniya, da kuma kamfanoni da su kafi biyan albashi mai tsoka. A shekarar 2016 kamfanin ya fitar da wasu ayyuka da sukafi kasuwa da yawan bukatar mutane da suke da kwarewa a wannan bangaren na aikin.
Akanyi amfani da wasu mizani wajen tantance wane aiki yafi soyuwa, da kuma zama mafi kasuwa. Ana duba yadda guraben aiki ke da yawa a wannan aikin, kamar ace mutun nawa suka samu aiki a irin wannan bangaren. Haka akan duba irin muhimanci wannan aikin ga rayuwar bil’adam.Cikin wadanda aka fitar a wannan shekar, daga na farko zuwa kasa, aikin tsara yadda na’urar kwamfuta ta ke aiki “Software architect” a turance, wanda akan samu gurabe sama da 653 kana albashi kan fara daga $130,000 dai-dai da naira milliyan 26,000,000, sai aikin inginiyan wuta “Electric Engineer” a turance, wanda akan samu gurabe sama da 2,516 kana albashi kan fara daga $76,900 dai-dai da naira milliyan 16,000,000.
Na uku kuwa shine aikin taimakon likita da mara lafiya “Nurse Practitioner” a turance, wanda akan samu gurabe sama da 5,624 kana albashi kan fara daga $99,500 dai-dai da naira milliyan 20,000,000. Sai aikin gine-gine da yin hanyoyi “Construction” a turance, wanda akan samu gurabe sama da 1,100 kana albashi kan fara daga $78,000 dai-dai da naira milliyan 16,000,000, sai aikin bada shawarwari ga jama’a dangane da wasu ayyuka da suka shafi rayuwar su “Consultant” a turance, wanda akan samu gurabe sama da 1,100 kana albashi kan fara daga $84,000 dai-dai da naira milliyan 17,000,000.
Sai aikin ma’aji na kamfani ko gwamnati “Technical Accountat” a turance, wanda akan samu gurabe sama da 1,100 kana albashi kan fara daga $70,000 dai-dai da naira milliyan 14,000,000, da aikin tsare-tsare na yadda za’a gudanar da harkokin kasuwanci “Stratefy Manager” a turance, wanda akan samu gurabe sama da 650 kana albashi kan fara daga $130,000 dai-dai da naira milliyan 26,000,000. Don haka akwai bukatar matasa idan zasu shiga jami'a sai su fara tunanin mai zasu karanta don neman aiki mai saukin samu da kuma samun albashi mai tsoka.