Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Badan Kudi Nake Bugawa Najeriya Wasa Ba Inji -Sylvester Igbonu


Shahararren dan wasan kwallon kafar nan na Super Eagles Sylvester Igbonu ya ce badan kudi yake bugawa kulob din na Super Eagles wasa ba, dan wasan ya bayyana cewa idan za’a bi nashi ra’ayin, kada Najeriya ta cigaba da ba duk wani dsan wasan kwallon kafa kudi.

Dan wasan wanda ke bugawa kulob din FC wasa ya baro kasar Denmark zuwa Najeriya ne domin bugawa kungiyar ta Super Eagles Wasa, amma ya ce bazai tabab juya wa duk wani kira daga kungiyoyin kwallon kafa na wasu kasashe baya ba domin ta nan yake samun kudaden shigar sa, dan wasan ya kara da cewa samun damar sa rigar ‘yan wasan Na Super Eagles ya wuce wasa.

Igbonu ya kara da cewa yayi mamaki matuka da ya karanata labaran irin abubuwan da ke wakana a kungiyar ‘yan wasan a yanzu, ya kuma kara da cewa babu yadda za’a yi ya hada darajar kasar sa da kudi, ya ce “Najeriya kasa ta ce dan haka tafi karfin kudi a wuri na”.

“Bugawa Najeriya wasa wata gagarumar dama ce dan haka me zai sa in sa tunanin kudi a zuciya ta? Ko naki ko naso kasa ta ce kuma nag ode wa Allah da yasa bani da matsalar kudi, kuma ina mai alfahari da damar da na samu domin bugawa kasa ta wasa".

Daga karshe ya nuna godiyarsa ga hukumar wasan kwallo ta Najeriya NFF musamman domin damar da ta bashi na bugawa kasar wasa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG