Tun bayan cire tallafin man-fetur a Najeriya, farashin kayan masarufi su ka fara tashi abun da ya sa rayuwa ta kara kunci ga matane da dama kuma ganin yanayin kuncin rayuwar ne ya sa gwamnatin tarayya ta sanar da samar da tallafin kudi naira miliyan dubu biyar da kuma kayan abunci ga kowacce jahar a Najeriya domin tallafawa talakawa, sai dai kuma majalissar Malaman addinin Musulunci a Najeriya ta ce wannan hanyar ba za ta bulle ba.
Farfesa Mohd Sadiq Abubakar Alkafawi shine babban sakataren majalissar na Kasa, kuma ya ce idan gwamnati na son tallafawa talakawa to ta bi tsarin tsohon shugaban kasa Sani Abacha amma ba ta hannun gwamnoni ba.
Sheik Yusuf Abdullahi Mafara shine mai-binciken kudi na majalissar Malaman ta Kasa kuma ya ce babbar mafita kan kuncin rayuwar talaka a Najeriya ita ce gwamnati ta maida farashin man-fetur yadda ta same shi.
Sheikh Mafara ya ce sauke farashin man-fetur ne kawai zai rage radadin kuncin rayuwa a Najeriya ba wai tallafi ba.
Taron majalissar Malaman addinin Musuluncin dai ya tattauna akan batutuwan da su ka hada da amfani da sulhu a Jamhuriyar Nijer, da bukatar rage kudin aikin hajji a Najeriya da kuma tsadar rayuwa. Dama dai tsadar rayuwar ta tunzura wasu mata da yara da su ka yi zanga a karamar hukumar Igabin jahar Kaduna.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5