Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Ba Kowacce Jiha Tallafin Naira Billion 5


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin tarayya ta amince da ba kowacce jiha da kuma babban birnin Tarayya tallafin naira biliyan 5 domin rage radadin cire tallafin man fetur.

An cimma wannan matsaya ne a wani taro na baya-bayan nan na Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC), wanda Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya jagoranta

Yayin wata tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin da ke Abuja, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana wannan muhimmiyar matsaya.

Gwamna Zulum ya ce gwamnonin za su sayi buhun shinkafa 100,000 da na masara 40,000 harma da takin zamani a rabawa talakawa da al'umma baki daya domin rage masu radadin da ake fama dashi na cire tallafin mai wanda ya haifar da hauhawan farashin kaya a kasa.

Gwamnan Borno Babagana Zulum
Gwamnan Borno Babagana Zulum

Ya kuma bayyana muhimman batutuwan da aka yi a yayin taron. Gwamna Zulum ya kara da cewa, Majalisar ta amince baki daya ta ba da karin tallafi ga jihohin da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar. Manufar ita ce a samar musu da karin ababen more rayuwa, da nufin kula da kwararar ‘yan gudun hijira daga makwabciyar kasa mai fama da matsaloli da suka shafi juyin mulki da halin da kasar ta Nijar ke ciki a yanzu.

Mambobin majalisar ta tattalin arziki na kasa sun hada da gwamnonin jihohi 36 na tarayya, tare da ministocin babban birnin tarayya Abuja, da na kudi, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), da kuma babban jami’in gudanarwa na kungiyar ta Najeriya ta kasa. Kamfanin albarkatun mai na NNPCL.

Wannan yunƙuri da matakan da gwamnati ta dauka ya nuna himmar gwamnati don magance ƙalubalen da ke tattare da cire tallafin man fetur da kuma tasirinsa, to amma sai dai wasu daga cikin 'yan kasa na ganin a baya an sha yin tallafi makamancin wannan amma kuma bai cika zuwa wajen talaka ba.

~ Yusuf Aminu Yusuf~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG