Gwamnatin kasar Mauritania ta ce an kashe mayakan al-Qaida 15, an kama wasu 9 a cikin wani samamen hadin guiwa da Mali wanda aka kai har wani sansanin ta'addancin al-Qaidar da ke Mali.
Wani Kanal din soji ya fada a jiya Lahadi cewa an kashe sojojin Mauritania biyu ma a cikin harin na ranar Jumma'a da aka kai sansanin yankin gandun dajin Wagadou dake daf da kan iyakar Mali da Mauritania.
Ya ce haka kuma sojojin Mali sun kama mayakan al-Qaida 9.
Sojojin kasashen biyu, wato Mauritania da Mali, su ne su ka kaddamar da samame da nufin yin turnukun kakkabe 'yan al-Qaidar kasashen Musulmin arewacin Afirka daga sansanonin su da ke daf da yankunan kan iyakokin kasashen.
'Yan ta'addan reshen kungiyar al-Qaidar arewacin Afirka na yin amfani da sansanonin su na kai hare-hare a yankin.