Wata kotun Majalisar Dinkin Duniya ta yankewa wata tsohuwar ministan kasar Rwanda hukumcin daurin rai da rai sabili da rawar da ta taka a kisan kiyashin da aka yi a kasar cikin shekara ta dubu da dari tara da casa’in da hudu. Kotun ta Tanzaniya da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya, ta yankewa Pauline Nyiramasuhuko hukumci yau jumma’a dangane da aikata laifukan kisan kare dangi, da hada baki a aikata kisan kiyashi da fyade da ake tuhumarta a kai. Ta kasance mace ta farko da kotun ta samu da laifi. Myiramasuhuko tsohuwar ministar iyali da harkokin mata ce lokacin da aka kashe kimanin ‘yan kabilar Tutsi da ‘yan Hutu dubu dari takwas a tsawon watanni uku. Ana zarginta da bada umarni da kuma taimakawa a yi wannan aika-aikar a yankin Butare dake kudancin kasar yayin kisan kiyashin. Kotun ta kuma yankewa danta Arsene Shalom Ntahobalim daurin rai da rai sabili da aikata irin wadannan laifukan. Yayinda aka yankewa wadansu jami’an hukumci tsakanin shekaru 25 a gidan yari zuwa daurin rai da rai
Wata kotun Majalisar Dinkin Duniya ta yankewa wata tsohuwar ministan kasar Rwanda hukumcin daurin rai da rai sabili da rawar da ta taka a kisan kiyashin da aka yi a kasar cikin shekara ta dubu da dari tara da casa’in da hudu.