Sama Da Kashi 40 Cikin 100 Na Mata Na Fuskantar Cin Zarafi A Yanar Gizo

A cewar kungiyoyin kare ‘yancin dan Adam cin zarafi da ake fuskanta kullum a yanar gizo shi ke matsawa mata da ‘yan mata yin taka tsan-tsan a kafafen sada zumunta.

Kusan mace daya cikin hudu a Burtaniya da Amurka, da sauran wasu kasashe shida, sun fada a wani binciken jin ra’ayin mutane cewa sun fuskanci cin zarafi a yanar gizo.

Sama da kashi 40 cikin 100 sunce cin zarafin ya saka su cikin zullumi da tsoro a rayuwarsu, yawancinsu kuma sun bayyana cewa suna samun matsala wajen barci, bayan sun fuskanci cin zarafin. A cewar kungiyar rajin kare 'yancin dan Adam ta Amnesty International.

Kungiyar ta kara da cewa kashi 75 cikin 100 na matan sun daina bayyana ra’yoyinsu a kafafen sadarwa, sun kuma cire kansu daga duk wata hira da jama’a.

Cin zarafin yanar gizo da ya hada da rubuta sharhi kan hotuna ko yin wasu kalaman batsa, na koyawa kananan yara darasin cewa ba laifi bane mutum ya aikata hakan.

Akwai bukatar gwamnati da kamfanoni su tashi tsaye domin tabbatar da cewa kafafen sadarwa ba gurin cin zarafi bane.

Your browser doesn’t support HTML5

Sama Da Kashi 40 Cikin 100 Na Mata Na Fuskantar Cin Zarafi A Yanar Gizo