Murtala Abdullahi (Dan Sudu Kurna) mawakin fadakarwa ne da suka danganci yanayin kasa da nusar da jama’a hanyar gudanar da rayuwarsu, a turba mai kyau da inganci.
Ya kara da cewar wakarsa na hasashe ne akan wasu abubuwa da ka iya kawo cikas ga rayuwa, a inda yake kwaikwayon mawaka kamar su Sa’adu Zungur wanda suke wakokin zube mai dauke da darussa da dama.
Dan Sudu, ya kara da cewar a wakokinsa akwai wacce yayi wa kasar Najeriya, inda yake nuni da dawowar demokradiya, da yadda yan siyasa wasunsu ke yaudara da yadda wasu ke da muradin cigaban kasa.
Wakokin shi dai na bayyanar da illolin rashin cika alkawari, karya da zamba cikin amince, kana wakokinsa na tattare da kafiya domin a cewarsa shine salonsa, ya cigaba da cewa yanzu ana rayuwar cin amana da karya wanda dole ne sai an fadakar da al’umma ire-iren wadannan matsalolin.
Dan Sudu, ya ce yakan kuma gabatar da wakokin hadin kai tsakanin kabilu, domin tabbatar da zaman lafiya a Tsakani. Babban burinsa dai bai wuce ya karanci aikin jarida ba, duk kuwa da cewar a da ya karanci fannin shari’a ne amma a yanzu yana da muradin canza sheka.