Yahaya Sabo Abubakar wanda aka fi sani da Yahaya 2K matashin mawaki wanda ya ce yana waka ne domin fadakar da matasa da su tashi tsaye su dogara ga kansu kuma yanzu lokaci ne da ya kamata su tashi tsaye su kama sana’ar hannu wato fannin noma.
Matashin ya bayyana cewa a cikin wakar sa ” ladan gona" ya isar da sakon muhimmancin auren zumunci a tsakanin al’umma, al’adar da ake daina raya ta.
Yahaya ya ce yana yin wakokin shi ne domin fadakarwa da wa’azantarwa, kuma yana hadawa da wakokin soyayya da kuma hip-hop.
Ya kara da cewar ya isar da sakon muhimmancin ilimi a wata wakarsa ta matasa mu koma makaranta domin magance matsalolin dake ciwa kasar mu tuwo a kwarya.
Yahaya 2K ya ce babban abinda ke ci masa tuwo a kwarya shine yadda yake ganin wasu matasa basu ga tsuntsu basu ga tarko inda suke garanbawul suna yawo ba tare da wani kwararren sana’a ko aiki ba.
Saboda haka ne yafi maida hankali wajen fadakar da matasa muhimmanci gudanar da sana’ar hannu.
Facebook Forum