Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutunmutumi Zai Zama Amsa Ga 'Yan-Mata A Rayuwa Nan Gaba Kadan


A nan da ‘yan shekarun gaba kadan, rayuwar yau da kullun zata ta’allaka kacokam akan mutunmutumi ‘Robot’ wanda mutane baza su iya gudanar da wata rayuwar su batare da mua’amala da robot ba.

Hasashen Hayliee Tat, matashiya mai shekaru goma sha daya 11, dake makarantar sakandire a jihar California ta kasar Amurka. Tana hangen cewar zamani na canzawa dai-dai da yadda lokaci yake.

Don haka a nan da ‘yan shekaru rayuwar yau da kullun zata koma sai mutane sunyi mu’amala da neman taimakon mutunmutumi, hakan yasa ta canza tunani don neman ilimin kerawa da sarrafa mutunmutumi.

Ta halarci wani taron karama juna sani da aka gudanar a Jami’ar California, wanda aka tara yara ‘yan makarantar firamari da sakandire don ilmantar da su muhimmancin sanin makama kere-keren mutunmutumi.

Tace “babu ‘yan mata da yara da dama a cikin fannin ilimin kera robot” don itama bata sanin ba, sai bayan gayyatar ta da akayi, wajen wani taron kera robot, daga bisani ta samu sha’awar zurfafa bincike, inda ta iya gano cewar tobot zai iya taka muhimmiyar rawa a rayuwar mutane ta yau da kullun.

Wanda take ganin cewar akwai bukatar matasa su tashi tsaye wajen neman ilimin kirkirar roboto, da kuma sanin hanyoyi da za’a sarrafa shi tare da bashi umurni wajen aiki kowane iri da mutun kan iya yi.

Matashiya Tat, ta kara da cewar, zuwa duk wani taron karama juna sani wanda ya shafi yadda ake kirkira da sarrafa robot musamman ga matasa yana da muhimmanci, domin kuwa ta nan matasa zasu hadu da wasu masu hazaka don karama juna fahimta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG