Salah, Mane Sun Shiga Cikin Masu Neman Kambun Zakaran Dan Wasan FIFA

Salah da Mane

‘Yan wasan Liverpool Mohamed Salah da Sadio Mane sun shiga jerin ‘yan wasa 11 da ke neani kambun zama zakaran duniya na FIFA a bangaren maza.

Wasu na hangen dan wasan Bayern Munich Robert Lewandowski ne zai karbi kambun bayan da ya taimakawa Bayern ta yi zarra har sau biyar a kakar wasanni, inda ya zamanto dan wasan da ya fi zira kwallo a gasar Bundesliga da kuma ta cin kofin Zakarun nahiyar turai UEFA.

Salah da Mane sun taka muhimmiyar rawa wajen lashe kofin gasar Premier League ta Ingila da Liverpool ta yi a kakar wasa ta 2019-20, wacce rabon da ta lashe tun a shekarar 1990.

Shi dai Salah dan asalin kasar Masar, ya zira kwallo 23 a wasanni 48 da ya bugawa Liverpool a gasa daban-daban a kakar wasan da ta shude.

A nashi bangaren, Mane wanda dan asalin kasar Senegal ne, ya zira kwallo 22 a wasanni 47 da ya buga.