Kwamitin da’ar ma’aikatan FIFA, shine ya fitar da wannan hukunci a yau Litinin, bayan ya samu Ahmed da take dokokin aiki da hukumar FIFA ta gindaya, ciki har da rashin biyayya da bayarwa da kuma karbar kyautuka da amfani da mukaminsa ta yanda bai dace ba da kuma yin sama da fadi da kudade.
Dakatar da Ahmad ya biyo bayan binciken da aka gudanar game da halayensa a matsayinsa na shugaban hukumar kwallon kafar Afrika daga shekarar 2017 zuwa 2019 da wasu harkokin da ya saka kansa a ciki.
Sakamakon hakan ne yasa aka dauki wannan mataki a kan dan shekaru 60 da haifuwar na haramta masa shiga harkokin kwallon kafa na cikin gida da waje tsawon shekaru biyar, yayin da kuma zai biya tarar CHF 200 000 (R3.3 million).
Sanarwar na zuwa ne wuni guda bayan da kwamitin da’ar ya samu shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Haiti kuma tsohon mamban kwamitin FIFA, Yves Jean-Bart, da laifin yin amfanin da mukaminsa ta yanda bai dace ba da kuma yunkurin yin lalata kana da laifin cin zarafin mata ‘yan wasa, wanda aka dakatar da shi harkokin wasan kwallon kafa tsawon rayuwarsa.