Ministan ya kuma yi alkawari sake gyara ofishin hukumar kwallon kafar kasar domin ya iya biyan bukatun mutane.
Da yake jawabi a kan wasanni biyu a jere da Najeriya ta yi da kasar Saliyo na neman gurbin gasar cin kofin Afrika da tawagar Najeriyar bata burge ba, ministan da ya roki afuwa daga ‘yan Najeriya a kan rashin kokari ‘yan wasan Super Eagle, ya ce sakamakon wasannin sun nuna muhimmancin yin gyare gyare cikin gaggawa, yana mai cewa jami’an kungiyar da koci Grenot Rohr ke jagoranta ba zasu iya biyan bukatun ‘yan Najeriya.
Dare ya ce, “haka wasa yake, wani loakci sai ya fitar maka da sakamako da baka da zaton sa.” Ya ce mun yarda da kwarewar ‘yan wasan Super Eagles. Tawagar zata gyara kura kuran ta.
Sai dai Dare ya yi watsi da batun da ake fadi cewa ba zai iya shiga cikin harkokin Super Eagles ba saboda akwai jami’an da aka zabe su domin gudanar da harkokin kwallon kafa a kasar.
A cewar ministan, a matsayin sa na wwanda aka damkawa amanar harkokin wasannin kasar, yana da ikon yin gyara idan ya gano ana samu kura kurai a kowane fanni wasa, har da na kwallon kafa.
Ya kara da cewa, Super Eagles tana wakiltan Najeriya ne, tana rera taken kasar Najeriya kana tana amfani da sutura masu launin tutar Najeriya, ya ce inda babu Najeriya a matsayin ta ta kasa mai cin gashin kanta, da babu wanda Super Eagles zata wakilci.