Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta ce ana kara samun masu aikata wannan muguwar dabi'a a arewacin Najeriya.
Matsalar shan miyagun kwayoyi ta jima tana addabar jama'a a Najeriya tare da yin mummunar illa musamman tsakanin matasa wadanda sune ake sa ran su zamo shugabannin gobe.
Daidai lokacin da lamurran siyasa suka soma gadan-gadan a dayan bangaren su kuma wuraren shan miyagun kwayoyi na ci gaba da samun sabbin mashaya, kamar yadda a jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi ta dira a wasu daga cikin wuraren shan kwayoyi.
A hirar shi da Muryar Amurka, kwamandan hukumar a jihar Adamu Iro Muhammad yace sun damke matasa maza da mata da yawan su ya kai 28 a samamen da suka kai.
Yace wuraren da ake magana sune daba inda ake taruwa ana shaye-shaye nan ne ake haduwa a shirya inda za'a je ayi sace-sace, garkuwa da mutane, da abubuwan da doka ta hana, saboda haka dole ne a hada hannu a tashi da gaske saboda a samu raguwar wannan abin.
"Jami'an hukumar sun yi samame a wuraren da ake shaye-shaye an kama matasa majiya karfi wadanda ya kamata su kasance masu amfani ga al'umma, har an kama wasu suna shan shisha, kuma an kama ‘yan mata da yawa matasa wadanda ya kamata ace suna hannun iyayen su a daidai wannan lokaci, kuma wadannan shaye-shaye sune ke kawo matsalar rashin tsaro a Najeriya."
Wasu daga matasan da aka kama sun nuna nadamar su a fili, duk da yake sun yi ikirarin suna sha.
Wani abu da jama'a suka jima suna korafi akai shi ne rashin hukumta wadanda ake kamawa da laifuka a Najeriya, sai dai akan batun shan kwayoyi kumandan yace suna wayar da kan masu shan kwaya bisa ga rashin sanin lahanin ta, kamar yadda ya gudana gaban manema labarai.
Sha da safarar miyagun kwayoyi dai na daga cikin abubuwan da suka jefa Najeriya cikin mawuyacin hali, wanda samun raguwar su kan iya ceto kasar daga wasu matsaloli.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5