Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miyagun Kwayoyi Na Ci Gaba Da Hallaka Matasa A Najeriya


Shan Miyagun Kwayoyi: Wani Yaro Na Shakar Gam Don Maye
Shan Miyagun Kwayoyi: Wani Yaro Na Shakar Gam Don Maye

A Najeriya alamu na nuna cewa duk fafatukar da hukumomi da wasu kungiyoyi ke yi wajen hana shan miyagun kwayoyi, har yanzu da sauran aiki gaba.

KEBBI, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da iyalan wani matashi a Jihar Kebbi, dalibi a kwalejin kimiyya da fasaha ta Waziri Umaru mai suna Musa David, ke zaman makoki akan kashe kansa da ya yi sanadiyyar yanayin da ya shiga bayan shan miyagun kwayoyi.

Matsalar sha da safarar miyagun kwayoyi ta jima tana ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya daidai lokacin da mahukunta da ma wasu kungiyoyin sa-kai ke fafatukar fadakar da jama'a akan illolin wannan mummnar dabi'ar.

A Jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya jama'a sun ga daya daga cikin illolin wannan mummunar dabi'ar lokacin da wannan matashi ya bakunci lahira sakamakon halin da ya shiga bayan shan miyagu kwayoyi.

Hukumar tsaron ‘yan kasa ta Civil Defense wadda a hannun ta matashin ya soma magagin mutuwa, ta ce ba kama shi ta yi da laifi ba, iyayen sa ne suka nemi taimakonta, bayan da suka lura da mummunan halin da ya shiga bayan miyagun kwayoyin da suke tuhumar ya sha.

Mu'awuya wanda yake mataimakin kakakin rundunar a Jihar Kebbi ya yi magana da yawun kakakin Abdulhakeem Adeyemi. Ya ce David Musa ya yi shaye-shaye ne ya fita hayyacinsa har ya soma ikirarin shirin hallaka wasu daga cikin danginsu, ganin haka ne ya sa dan uwansa Daniel Samuel Galadima ya nemi taimakon hukumar domin a samu ya dawo hayyacinsa.

Wasu daga cikin miyagun kwayoyi da hukumomi suka kwato a hannun masu safarar miyagun kwayoyi
Wasu daga cikin miyagun kwayoyi da hukumomi suka kwato a hannun masu safarar miyagun kwayoyi

Ya ce bayan an kawo shi ofishinsu sun soma kulawa da shi kuma ya fara dawowa hankalinsa har ya nemi afuwa, daga baya ya bukaci a bashi dama ya je makewayi, aka hada shi da jama'i daya suka je, daga nan sai jami'in ya ganshi ya fito a guje da jini ya rike wuya.

A lokacin da hukumar tsaron ke kokarin wanke kanta daga mutuwar Musa David wanda ya rasu bayan an kai shi asibitin Sir Yahaya dake cikin garin Birnin Kebbi, su kuwa dangin mamacin sun ce duk da yake ba kama shi da laifi hukumar ta yi ba, amma dai sun ga sakacin ta bari har ya jefa kansa ga halalka.

Mrs. Tina Augustin gwaggon mamacin ta ce inda suka ga laifin hukumar shine rashin saka masa sarka a hannu ko kafa su daure shi, saboda sun ga mummunan halin da ya kwana ciki, amma kuma dangin sun lura da watakila jami'an basu daure sa ba saboda suna ganin ba tuhumar sa ne suke yi ba.

Yayinda jama'a ke garzayawa gidan mamacin domin ta'aziya, masu sharhi akan lamurran yau da kullum na ganin akwai saura ga fafatukar da ake yi wajen ilmantar da jama'a akan wannan mummunan dabi'ar, yayinda iyaye suma ya dace su kara sa ido ga yaron su.

Farfesa Tukur Muhammad Baba na daga masharhantan wanda ke ganin ita ma gwamnati akwai abinda ya dace ta kara yi don maganin wannan matsalar.

Ya ce kamata ya yi gwamnati ta samar da ayukkan yi ga jama'a ta yadda matasa zasu samu abin yi don rage zaman banza, su kuwa mahukunta su dage tare da yin gaskiya wajen yaki da mummunar dabi'ar yadda ya kamata.

Matsalolin sha da safarar miyagun kwayoyi dai sun hallaka jama'a da dama a Najeriya duk da kokarin da mahukunta ke yi na magance matsalar.

Saurari rahoton Muhammad Nasir:

Matsalar Sha Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Najeriya Na Ci Gaba Da Halaka Rayuwar Matasa .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

XS
SM
MD
LG