Sakataren Tsaron Amurka Ya kai Ziyara Israila

Ash Carter sakataren tsaron Amurka

Biyo bayan yarjejeniya da aka cimma da kasar Iran akan shirin nukiliyarta sakataren tsaron Amurka ya kai ziyarar kwantar da hankalin gwamnatin Israila

A mataki na farko, Sakataren Tsaron Amurka Ash Carter ya kai ziyara Isra’ila, domin ganawa da kawayen Amurka da ke yankin, kan matsayar da aka cimma game da batun nukiliyar Iran, da kuma yakin da ake yi da mayakan kungiyar IS.

A yau Litinin Carter ya hadu da Ministan Tsaron Isra’ila Moshe Yaloon, inda suka yi tattaki zuwa arewacin kasar domin ganin halin da ake ciki a kan iyakar Isra’ila da Lebanon.

A gobe Talata ake kuma sa ran Carter zai gana da Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ke adawa da shirin nukiliyar Iran da kuma matsayin da aka cimma, lamarin da ya kwatanta a matsayin “kuskure ne mai cike da tarihi.”

Mr Carter dai ya ce bashi da niyyar ya sauya matsayar da Netanyahu ya zauna a kai, yana mai cewa za su tattauna game da tsare-tsare da suka danganci kasashen biyu.