Sanarwar da ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ta bayar, ta nuna cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson zai fara da ganawa ne da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ranar Talata.
Wannan ziyarar ta Tillerson ita ce ta farko da wani babban jami'in gwamnatin Amurka zai kai Najeriya tun lokacin da Shugaba Donald Trump ya dare kan shugabancin Amurka.
A lokacin ganawar ana sa ran zasu tattauna akan batun yaki da ta'addanci da yanzu haka Najeriya ke samun tallafi daga kasar ta Amurka.
Wasu masana sun yi tsokaci akan yadda suke ganin ziyarar ta Rex Tillerson. Ta fuskar tattalin arziki Dr. Muhammad Kontagora, wani masanin tattalin arziki ya ce da dadewa kasashen biyu nada huldar cinikayya tare. Ganin yadda kasashen Afirka ke maida hankali da yin hulda da China ya tada kishi. Kasashen Afirka dai na kyautata zaton karkata zuwa kasar China zai taimakawa tattalin arzikinsu saboda taimako da take bayarwa tare da horo.
Shi ma Malam Musa Jika na kungiyar Amnesty Support Group dake fafutikar kare 'yanci a Najeriya yana ganin lokaci ya yi da 'yan siyasa zasu tashi tsaye saboda duk abun da su key ana ganinsu. Misali, Amurka ta ce zata ido akan zaben Najeriya na shekara mai zuwa. Wannam alama ce har yanzu Amurka bata yadda da hukumomin Najeriya ba, inji Jika.
Ya ci gaba da cewa ziyarar zata taimaki 'yan Najeriya da 'yan siyasa s yi karatun ta natsu saboda duk abun da su keyi ana kallonsu musamman shi shugaban kasa da ake ganin zai tsayatr da gaskiya da adalci amma kuma sai ya zama ba haka ba.
Ga rahoton Babangida Jibrin dakarin bayani
Your browser doesn’t support HTML5