Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tilleron Ya Yabawa Shirin Hadin Kan Kenya


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson, tare da Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson, tare da Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya fada a jiya Juma’a cewar sasantawar siyasa tsakanin shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da madugun 'yan adawan kasar Raila Odinga, wata babbar nasara ce ya kuma kara da cewa Amurka tana bada goyon bayanta ga hadin kan kasar da ci gaban demokaradiya.

Kenyatta da Odinga sun gana a karon farko, tun bayan zaben shugaban kasa da aka yi a bara mai tattare da takaddama, a wani matakain da suka kira tafiya tare domin hadin kan kasa.

Tillerson ya yabawa matakin hadin kan a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da yayi da ministan harkokin wajen Kenya, Monica Juma a birnin Nairobi

Wadannan shugabannin biyu sun nuna dattaku, wurin sanya hannu a kan wata yarjejeniya a jiya, inji skatare harkokin wajen Amurka. Yace Amurka tana zuba ido ta taimakawa aiwatar da shirin da aka sanar da safiyar jiya don kawo hadin kai da kuma magance duk wata rarraba da kasar ke fama da ita.

Babban jami’in diplomasiyar Amurkan ya nanata muhimmancin walwalar 'yan jarida a cikin harkar demokaradiya kuma ya gargadi gwamnati ta sakarwa kafafen yada labarai mara su yi aikinsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG