Sakataren Harkokin Wajen Amirka John Kerry Zai Kai Ziyara Najeriya

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry zaiyi bulaguro zuwa Nigeria domin ganawa da manyan yan takarar shugaban Nigeria guda biyu da kuma yin kira ga ganin cewa an gudanar da zaben da za'a yi a watan gobe cikin yanci da adalci.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry zaiyi bulaguro zuwa Nigeria domin ganawa da manyan yan takarar shugaban Nigeria guda biyu da kuma yin kiran, ganin cewa an gudanar da zaben da za'a yi a watan gobe cikin yanci da adalci.

Jiya Juma'a ma'aikatar harkokin wajen Amirka tace gobe Lahadi idan Allah ya kaimu John Kerry zai tafi birnin Ikko idan zai jaddada muhimmancin tabbatar da an gudanar da zabe cikin lumana kuma sahihiya.

John Kerry zai gana da shugaba Goddluck Jonathan da kuma Janaral Muhammadu Buhari dan takarar shugaba na jam'iyar APC.

Zabubbukan da aka yi a baya sun fuskanci tarzoma. Nasarar da shugaba Jonathan ya samu a zaben da aka yi a shekara ta dubu biyu da goma sha daya da aka yi rikici akan sakamakonsa ya hadasa tarzoma a arewacin kasar harma aka kashe kimamin mutane dari takwas.

Zaben na bana zai fuskanci sarkakiya a saboda hare haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa, wadda tuni ta kashe dubban mutane a arewa maso gabashin Nigeria kuma yanzu haka tana mamaye da yawancin kananan hukumomin jihar Borno.

Jami'an Nigeria sunce za'a gudanar da zaben, a ranar sha hudu ga watan gobe na Fabrairu idan Allah ya kaimu kamar yadda aka shirya.