Wannan nasara ta Abuja ta sanya wakilin Hama Amadou wato Alhaji Ibrahim Muhammad zumudi, inda yace, kama dan takarar su da akayi shine ke kara masa farin jini domin ya samu irin wanda bai taba samu ba. hakan ne yasa magoya bayan Hama ke ganin daga gidan yari sai gidan shugaban kasa.
Shi kuma Mustapha Haruna wakilin MNSD ya nuna gamsuwa ga wannan zaben, inda yace tabbas jam’iyyar LUMANA tayi abinda ya kamata domin ta aiko wakilan ta zuwa Najeriya, domin suyi tallar dan takararsu hakan kuma shine ya sa suka sami nasara.
Wakilin PNDS TARAYYA Alhaji Musa Na Kowa yace dan takarar su shugaba muhammadu Issoufou shine zai lashe zaben daga karshe.
Shugaban yan Nijar mazauna Najeriya, Abubakar Kalidu yace rashin samar da rijista kan lokaci shine ya sanya karancin masu jefa kuri’a a Najeriya, inda yake ganin a matsayin Najeriya baki daya ace mutane 6,300 ne kadai sukayi rijistar yin zabe, domin a Abuja kadai ma akwai yan Nijar 12,500, banda mutanen dake Lagos da Kano da Kaduna da Port Court da Jos. Mallam Kalidu dai ya baiwa gwamnatin Nijar shawarar idan za a yi zabe nan gaba a bada lokacin da ya kamata don mutane su sami yin rijista.
Cibiyar Abuja dake ofishin jakadancin Nijar, zata tattara sauran sakamakon yankuna shida da akayi zaben don bayar da sakamako na karshe.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5