Sakamakon Gasar Kamfanin Microsoft Ta Duniya

Microsoft Layoffs

Kamfanin Microsoft ya fitar da sakamakon gasar Amfani da Fasaha Don Kawo Sauyi ga matasa ta wannan shekarar. Gasar dai ta tambayi matasa daga duk fadin duniya da su rubuta masalaha kan yadda za’a iya yin amfani da fasaha wajen warware wata takamammiyar matsalar zamantakewar al’umma a inda matashin yake.

Saviour Okusenogu daga Lagos a Najeriya, na daga cikin matasan da suka sami nasarar lashe wannan gasar. A bayan Najeriya, sauran matasan da suka samu nasara sun fito daga kasashe kamar Chile, Ecuador, Greece, India, Nepal, Amurka da Uruguay.

Wadannan matasa da suka yi nasara, sun kasance wakilai na matasan da suka kuduri kawo sauyi mai amfani na zamantakewa a tsakanin al’ummarsu.

Saviour Okusenogu daga Lagos, na son kirkirar wata hanya da zata jawo hankulan yara ga ilimin kimiyya da aikin injiniya, ta hanyar samar da sabbin dabarun koyar da wadannan darussa cikin raha da gwaje-gwajen zahiri masu sha’awa, maimakon karatu kawai da ake yi na wadannan darussa a makarantun sakandare.

Zakarun wannan shekarar sun kirkiro hanyoyi masu karfi na warware matsalolin zamantakewa a fannoni da suka hada da ilmi, kimiyyar na’ura mai kwakwalwa da koyon aiki da na’urorin zamani.

Microsoft dai ya rabawa duk matasan da suka sami nasarar lashe gasar kudi Dala dubu biyu da dari biyar, kimanin Naira dubu 550, da basu na’ura mai kwalkwalwa ta taimaka musu wajen aikin su.