Sai Najeriya Ta Ci Bashi Kafin Ta Cimma Kasafin Kudinta Na Bana

Ministan Ma'adinai Kayode Fayemi

Ma'adinai ke samarda kashi 40 na kudaden shigar kasar Botswana

Biyo bayan faduwar farashi Mai a kasuwar duniya,Gwamnatin Taryyar Najeriya, sai ta ciwo bashin fiye da Naira miliyan 2,000, kafin ta cimma kasafin kudinta na wannan shekarar.

Kasar Botswana, ta shafe shekaru 20, tana habaka bangaren ma’adinai, yanzu ta gama kuma wannan bangare ne kadai ke samarwa kasar kashi 40, na kudaden shigar ta.

A cewar Alhaji Sani Shehu, shugaban kungiyar masu haku ma’adinai ta Najeriya, Najeriyar bata makara ba, yana mai cewa akwai kudade da aka ajiya na habaka ma’adinai a Majalisar kasa, yace idan aka yi abun da ya kamata za’a samu wannan kudin.

Ya kara da cewa akwai kudi na tallafawa Tama da Karafa shima yana nan saboda haka gwamnati ta natsu ta bincike wadannan kudade ta kammalasu idan akayi haka za’a samu mafita.

Ministan Ma’adinai, Dr. Kayode Fayemi, wanda yace ba’ayi wani hubbasan da zai sa a ci moriyar albarkatun da Allah ya horewa kasar ba, ya kara da cewa bashin da ‘yan Najeriya, ke binsu a halin yanzu shin tabbatar da an fara aikin cin moriyar albarkatun Ma’adinai dake karkashin kasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Sai Najeriya Ta Ci Bashi Kafin Ta Cimma Kasafin Kudinta Na Bana - 2'25"