Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Korafi kan Hana Amfani Da Katin ATM Na Najeriya A ketare


ኪም ዮንግ ያም
ኪም ዮንግ ያም

‘Yan Najeriya mazauna Amurka sun bayyana cewa, basu ji dadin shawarar da bankunan Najeriya suka yanke na hana ciniki da katunan bankin kasar a kasashen ketare ba.

Sun bayyana cewa, daukar wannan matakin zai janyo matsalar gaske musamman ga ‘yan kasuwa kasancewa, zamani ya kai wani matsayin da harkokin kasuwanci yafi karfi ta hanyar internet da ake gudanarwa da katunan.

Daya daga cikin wadanda Sashen Hausa ya yi hira da shi ya bayyana cewa, yanzu haka yana da wani bako daga Najeriya wanda ya shiga halin tsaka mai wuya, kasancewa an hana fitar da tsabar kudi, ya kuma shigo Amurka ya rasa yadda zai biya kudin Otel da yake an toshe damar amfani da katin daukar kudin.

Wannan dokar ta kuma shafi dalibai dake karatu a kasashen waje da matafiya, da duk wadanda ke fita kasashen waje domin wadansu dalilai da suka hada da neman jinya.

Sun bada shawarar cewa, ko da za a yi gyara bai kamata a yi kan mai uwa da wani ba. Kamata ya yi a duba a gani wadanda ya kamata wannan dokar ta shafa amma bai kamata a yi dokar da, a maimakon gyara zata jefa al’ummar kasar cikin wani mawuyacin hali ba.

Ga cikakken bayanin

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG