Sai da K'oshi Ake Samun Ci Gaba Inji Gwamna Wamako

Wani manomin Najeriya na aiki a wata gonar rogo

Gwamnatin jahar Sokoto ta gina cibiyoyin koyar da dabarun noma na zamani
A da can kafin a fara hakar man fetur, kasar Najeriya ta yi fice sosai saboda karfin tattalin arzikin ta, a bangaren aikin gona, wanda ko baicin samar da kashi saba’in cikin dari na ayyukan yi, haka kuma shi ne babbar hanyar samar da wadatar abinci ga ‘yan kasar su fiye da miliyan talatin a wancan lokaci. Sai dai daga aka fara samun man fetur aka wancakalar da noman,aka yi watsi da shi, al’amarin da ya haifar da gibin gaske ta bangaren rashin ayyukan yi musamman ma a arewacin kasar ta Najeriya, dalili kenan da ya sa gwamnatin jahar Sokoto ta giggina manya-manyan cibiyoyin samun horon dabarun ayyukan gona na zamani guda uku, daya-daya a kowace mazabar dan majalisar dattawa domin taimakawa ‘yan jahar su karu da dabarun noma na zamani da kiwon kifi da kaji da shanu da kuma sarrafa abincin su da dai sauransu, duka wannan da burin samar da karin ayyukan yi da dogaro da kai ga jama’ar jahar ta Sokoto. Wakilin Sashen Hausa a jahar Sokoto, Murtala Faruk Sanyinna ya ce tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida ne ya kaddamar da daya daga cikin cibiyoyin, shi ma gwamnan jahar Sokoto Aliyu Magatakarda Wamako ya ce a kowace shekara ‘yan jahar Sokoto dubu tara ne za su samu horo a cibiyoyin, sannan ya ci gaba jawabi kamar haka:

Your browser doesn’t support HTML5

Jahar Sokoto ta gina cibiyoyin koyon aikin noma na zamani - 1:56