Sace daliban Cibok da 'yan Boko Haram suka yi ya zama lamarin da ya damu duniya gaba daya inda fadar shugaban Amurka tace lamarin bala'i ne na bacin rai.
WASHINGTON, DC —
A ranar Litinin mai magana da yawun fadar shugaban Amirka ta White House Jay Carney yayi Allah wadai da sace yan makarantar akan cewa bala’i ne na bacin rai.
Yace an sha yiwa shugaba Obama bayanin aukuwar wannan al’amari kuma masu lura da matakan tsaron cikin gidan na shugaban suna ta nazarin wannan al’amari kut da kut. Haka kuma yace ma’aikatar harkokin wajen Amirka tana tuntunbar gwamnatin Nigeria akan irin matakan da zasu dauka domin marawa yunkurin ganowa da kuma ceto wadannan ya matan.
Jay Carney yace tamakon dakile ta’adancin da Amirka zata baiwa Nigeria, sun hada harda musayar bayanai da inganta iyawar binciken Nigeria da kare farar hula da kuma tabbatar da cewa an mutunta yancin kowane mahaluki. Haka kuma Jay Carney yace suna kuma kokarin taimakawa rundunar sojan Nigeria inganta kwarewarta wajen kara sanin makamin aikinta da yadda zata kwance bama baman da aka yi niyar kai hare hare dasu da kuma yadda zata iya ganowa da kuma dakile aiyuka ko kuma hare haren ta’adanci.
Jay Carney yace Amirka wadda tuni ta ayyana kungiyar Boko haram a zaman kungiyar yan ta’adan kasa da kasa a bara, tana kuma goyon bayan shirye shiryen da aka tsara domin taimakon yankunan da suka fi fuskantar wannan barazana kara fahimtar masifar wannan kungiya.
A bayanin da aka yiwa yan jarida a ranar Litinin mai magana da yawur ma’aiktar harkokin wajen Amirka Marie Hart tace yunkuri na Amirka yana da amfani da kuma muhimmanci
Tace wadannan abubuwa ne da zasu taimakawa Nigeria a kokarin da take yi na gano inda aka kai wadannan ‘yan mata, wadanda bisa dukkan alamu kila yawancinsu an fitar dasu daga Nigeria. Da wani dan jarida ya nemi sanin shin wannan hasashe data yi ya ta’alaka ne akan bayanai da hukumomin Nigeria suka yiwa Amirka ne akan wannan al’amari, ko kuwa? Sai Marie Harta tace wannan hasashen ya ta’alaka ne akan yadda Amirka tayi nazarin al’amarin, Haka kuma tace Amirka na karfafawa gwamnatin Nigeria gwiwar data yi aiki da sauran kasashe makwaptanta, ta gani ko akwai matakan da zasu iya dauka tare domin ceton yan matan.
In dai ba’a mace ba, a sakon vidiyon da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya gabatar wa kamfanonin dilancin labaru, ya baiyana yan matan a zaman bayi kuma zai sayar dasu a kasuwa.
Sace wadannan yan mata yasa Senata Amy Kiobucher daga mazabar Minnesotta nan Amirka wadda a lokacinda tayi aikin gurfanar da masu laifi gaban kuliya, ta tinkari batutuwan da suke da alaka da fataucin mutane, tace irin wadannan aikata laifi na rashin imanin da tausayi yana bukatar su dauki matakai nan take na taimakawa wajen ceton yan mata a maida su gun iyayesun a kuma hukunta wadanda suka sace su. Haka kuma Senata Amy tayi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da yayi Allah wadai da sace ‘yan mata ya bukaci taimakon kasa da kasa domin a samu a ceci wadannan ‘yan mata.
Ga karin bayani daga Jummai Ali.

Your browser doesn’t support HTML5