Sabuwar Takaddama Tsakanin China Da Korea Ta Arewa

  • Murtala Sanyinna
Da alamu dai Pyongyang ta nuna rashin amincewa da shirin China na kafa kayayyakin da za su iya watsa shirye-shiryen rediyon FM zuwa Koriya ta Arewa.

Wata sabuwar alamar rashin jituwa ta kunno kai a alakar da ke tsakanin Koriya ta Arewa da China, dangane da shirin da Beijing ta yi na kakkafa cibiyoyin sadarwa a kusa da iyakarta, wanda masu sharhi ke ganin zai iya zama wata hanya da China za ta karfafa tasirinta a kan makwabciyarta ta kudanci.

Da alamu dai Pyongyang ta nuna rashin amincewa da shirin China na kafa kayayyakin da za su iya watsa shirye-shiryen rediyon FM zuwa Koriya ta Arewa.

Kafar yada labarai ta Kyodo ta ruwaito a wannan makon cewa, Pyongyang ta aike da sakon email na korafi game da shirin, zuwa ga hukumar kula da harkokin sadarwa ta Majalisar Dinkin Duniya wato ITU, tana mai cewa Beijing ba ta tuntube ta game da shirin ba kafin soma shi, wanda ya zama tamkar wani "karan tsaye" ne ga ka’idodin hukumar ta ITU.

An aike da korafin ne bayan da hukumar kula da harkokin sadarwa ta Majalisar Dinkin Duniya da ke samar da hanyoyin sadarwa a duniya, ta bankado wasu bayanai a watan Yuni, game da shirin kasar China na kafa cibiyoyin sadarwa 191, da za su iya watsa sakonnin radiyon FM, ciki har da tashoshi 17 da ke kusa da kan iyakar Koriya ta Arewa, a cewar Kyodo.

Pyongyang ta ce wadannan tashoshi 17, ciki har da ta birnin Dandong da ke kan iyaka, na iya haifar da "tsangwama mai tsanani."

Wani mai magana da yawun ITU ya shaidawa Muryar Amurka cewa "hukumar ba za ta iya tabbatar da ko ta sami korafin ba ko kuma a'a," domin "irin wannan korafi na iya ya kunshi bayanan sirri da ba a bukatar su kai ga kunnen jama'a, kuma yana iya kawo cikas ga tattaunawar bangarorin biyu."