Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barin Bakin Amaka Koma Baya Ne A Yunkurin Hada Kan Kasa-Yan Najeriya


Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)

‘Yan Najeriya mazauna kasar Kanada sun bayyana takaicin katobarar da wata mata da ake kyautata zaton ‘yar kabilar Igbo ce, dake da zama a Kanada Amaka Patience Sunnberger ta yi, inda aka ji ta tana cewa a zubawa ‘yarbawa da kuma ‘yan al’ummar yankin Benin guba a ruwa da abinci a duk inda su ke.

Kalaman na Amaka dai sun jawo ce-ce-ku-ce, wanda ya sa fitattun mutane ciki har da shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, suka bukaci mahukuntan Canada su gurfanar da ita a gaban kuliya, saboda saba dokokin kasa da kasa da na Canada.

Haka ma Majalisar tarayyar Najeriya ta bukaci hukumomin kasar Canada su bincika lamarin.

A hirarshi da Muryar Amurka, Dr Emma Eze wani dan kabilar Igbo mazaunin kasar Canada ya bayyana takaicin kalaman na Amaka, yace maganar abin dariya ne da ban takaici.

Yace "wannan bidiyon abin ban dariya ne, wadansu sukan yi wani abu sabili da kawai yadda suke ji a zuciyarsu. Ban ga dalilin da zai sa wani ya yi irin wannan bidiyon ba, domin kasancewa na fito daga Najeriya, dukanmu daya ne. Ni dan kabilar Igbo ne, kasancewa na fito daga najeriya na fi alaka ta kut da kut da wadanda ba ‘yan bakibalar igbo ba ne a nan. Galibin abokaina a nan yarbawa ne. Duk da yake wani lokaci mutum zai so ya rika mu’amala da ‘yan kabilarsu, amma hakan ba mai yiwuwa ba ne kowanne lokaci, kuma wannan ba zai sa wani ya yi tunanin cutar wata kabila ba. Menene ribar yin haka? A wuri na, dabbanci ne, musammam ma da muka kaura zuwa wannan kasar inda mu tsirarru ne ana ganinmu kawai a matsayin ‘yan Najeriya. Mutane basu da lokacin irin wannan hirar kasancewa a nan daga lokacin da mutum ya tashi da safe har lokacin da zai kwanta, yana tunanin yadda zai kashe wutar gabanshi ne."

Da take tsokaci kan batun, Tosin Adebayo, yar kabilar Yarbawa, daya daga cikin kabilun da Amaka ta ce a hallaka, ta ce, duk mai cikakken hankali da tunani ba zai yi irin wadannan maganganun ba. Bisa ga cewarta, zai yiwu akwai wani abinda ke damun matar da tayi wannan maganar, amma ba za a dauka tunanin ‘yan kabilar ke nan ba, domin akwai baragurbi a kowacce kabila.

"Muna tare shekara da shekaru, kuma bamu kula da banbancin kabila, wannan ya zo da mamaki. Gaskiya ne, akwai yarbawa da basu da kirki, kuma ni bayarbiya ce, haka kuma akwai ‘yan kabilar Igbo da basu da kirki, amma mun dade muna cudanya da juna. Idan muka bar Najeriya, muna ganin kanmu a matsayin ‘yan kasa daya. Ina da kawayen ‘yan kabilar Igbo. Babbar kawata Igbo ce, mun fara abota shekaru takwas da suka shige. ina da abokai Hausawa, bamu ganin kanmu da wannan tunanin. Abin takaici ne ganin yadda ta zo kasar nan da wannan tunanin."

Ita kuwa Shelni Pukuma ‘yar arewacin Najeriya dake da zama a Toronto, tana ganin idan ba a yi hankali ba, irin wannan maganar na iya shuka mummunan iri a zukatan yara masu tasowa.

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo
Kungiyar Ohanaeze Ndigbo

Tuni babbar kungiyar hadin kan ‘yan kabilar igbo, Ohanaeze Ndigbo ta nesanta kanta da wannan katobarar ta kuma yi allah wadai da ita.

A cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba, kakakin kungiyar na kasa Alex Ogbonnia ya bayyana cewa, maganar da Amaka ta yi tana da tada hankali sabili da haka ya zama dole kungiyar ta maida martani domin wanzar da zaman lafiya.

Yace ‘yan kabilar Ibo sun fi kowace kabila ta Afirka yawan tafiye-tafiye. Suna kuma maida duk inda suke gida, suna cudanya da al’ummar yankin, suna ba da gudummawa ga ci gaban duk inda suka samu kansu.

Yace “Ohanaeze tana amfani da wannan damar wajen wayar da kan matasa cewa, ‘yan kabilar Igbo, Edo, da Yarbawa suna da kamanceceniya da juna ta fannoni da dama. Kuma an dade ana auratayya tsakanin ‘yan kabilun Igbo, Yarbawa, da Edo da suka hayyafa suka kuma yi jikoki da suka zama mutanen kwarai a al’umma.”

Kungiyar hadin kan Yarbawa Afenifere
Kungiyar hadin kan Yarbawa Afenifere

Tun farko, bayan fitar wannan maganar ta Amaka, kakakin kungiyar hadin kan Yarbawa Afenifere na kasa Jare Ajayi, ya turashi ga takwaranshi na Ohanaeze Ndigbo ya kuma bukaci kungiyar ta dauki matakin gaggawa.

A jiya alhamis, Amaka ta sake wallafa wani sako a matsayin maida martani ga kiraye-kirayen da ake yi na neman hukumomin kasar Canada su dauki mataki a kanta, inda take cewa, ita ‘yar kasar Canada ce, kuma akwai banbanci tsakanin tsarin shari'a na Kanada da na Najeriya, da nufin cewa, paspo din kasar Kanada da ta mallaka, ya bata kariya daga kamawa ko fitar da ita daga kasar.

Saurari cikakken rahoton:

Barin Bakin Amaka Komawa Baya Ne Yunkurin Hadin Kan Kasa
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:06 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG